facebooktwitterinstagramgoogleplus


Home »; other »; news [news] Ahmad Makarfi ne halartaccen shugaban pdp
12-07-17 (12:37)
Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da Sanata Ahmed Makarfi a matsayin halattaccen shugaban jam"iyyar adawa ta PDP. Wannan hukunci na nufin bangaren Sanata Ali MOdu Sheriff ba za su iya daukaka kara ba. Shekara biyu kenan ana rikicin shugabanci a jam"iyyar wacce ta shafe shekara 16 tana mulkin kasar. Lamarin da raba kawunan "ya"yan jam"iyyar a sassan kasar daban-daban. Rahotanni sun ce jami"an bangaren Ahmed Makarfi da suka halarci zaman kotun, sun nuna farin cikinsu ga hukuncin. Sai dai kawo yanzu babu wani martani da ya fito daga bangaren Ali Modu Sheriff da suka sha kaye. Tuni wasu masu ruwa da tsaki a jam"iyyar suka yi maraba da hukuncin. Tsohon kakakin jam"iyyar Cif Olisa Metuh ya bayyana cewa babu wanda ya yi nasara ko ya fadi sakamakon hukuncin, yana mai cewa dama ce ta a hadu tare domin inganta jam"iyyar. A wata sanarwa da ya fitar, ya ce wajibi ne "mu sake bude kofa ga dukkan "yan Najeriya da ke son ganin tsarin demokuradiyya ya tabbata". Me ya raba PDP da APC? An dade ana zargin jam"iyyun siyasar Najeriya da rashin akida, inda suke mayar da neman mulki babbar munufarsu. A wata hira da BBC a kwanakin baya, tsohon shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta"annati, EFCC, Mallam Nuhu Ribadu, ya shaida wa BBC cewa babu wani cikakken banbanci tsakanin jam"iyyun PDP da APC.


Share Button

Post by admin
Post Category news