facebooktwitterinstagramgoogleplus


Home »; other »; films industry [Bollywood] Jarumi Saif Ali khan bayya farin cikin shigar yarsa film.
16-06-17 (11:29)
Yayin da sabuwar jaruma Sara Alikhan kuma yar jarumi Saif Alikhan take kan shirye shiryenta na fitowa a cikin film din ta na farko mai suna "Kedarnath" tare da Sushant Singh Rajput, da alamun Maman ta Amrita Singh na taimaka mata akan shirinta da ke yi, amma a bangaren Mahaifinta ba haka yake ba abun, duk da Shima dai Saif Alikhan Jarumin film ne sananne a duniyar fina finan bollywood na India hakan bai hana ya fito karara ya baiyyana rashin gamsuwar sa da zabin sana"ar da yar sa Sara ta yiba nayin film . Saif Alikhan yace duba da yadda Sara taje tayi karatu a Newyork mai zai hana ta tsaya can tayi aiki a Amurkan, yabayyana cewa bawai shi yana nufin ya raina sana ar film bane a"a, ko kadan amma fa bai zama lalle dan kana jin zakayi nasara ya zama dole kayi nasara ba. Wannan ba rayuwa bace da kowani iyaye zasu sowa "ya "yansu. Baban nata ya kara da cewa yar sa Sara ako da yaushe tana da burin kasan cewa jaruma, yace na tuna shekaru da suka wuce a baya lokacinda muke kan wani wasa a gidan wasa a gaban taron jama"a ni da Salman na ga Sara ta tsaya gefe tana kallon mu. Na gano cewa shine abun da take so ta tsaya kan dandamali jama"a na mata shewa ana kiran sunanta. Saif Alikhan yakara da cewa batare dashi suka zabar mata project dinta na film dinda zata fara ba, amma idan har tana da tambaya ko shawaran da take so zai iya taimakon ta akai, zamuyi magana akan film kamar yadda muke magana akan komai. Nasan abun da take yi kuma zamuyi magana akan film kamar yadda muke magana akan komai.
Kalli wasu hotunan Sara Alikhan
Yanzu dai Sara tana kan kimtsawa domin fitowa a film din Abhishek Kapoor"s Kanardath wanda aka shirya za"a yi a karshen shekaran nan.


Share Button

Post by admin
Post Category films industry